Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Waje-Rod Da Kasar Italiya


Kasar ta Italiya wadda take rike da kofin kwallon kafar duniya, da kuma wadda ta zo ta biyu a gasar a 2006, Faransa, duk za su koma gida tun a zagayen farko

Kasar da ta ke rike da kofin kwallon kafar duniya a yanzu haka, Italiya, ta sha kashi a hannun 'yan kasar Slovakia da ci 3 da 2, kuma a yanzu haka zata koma gida hannu wofi tun a zagayen farko.

Wannan nasara da Slovakia ta samu kan Italiya alhamis a birnin Johannesburg ya ba ta maki hudu a rukuninsu na 6 ko "F" a zagayen na farko, kuma zata haye zuwa zagaye na biyu.

A bayan da aka yi waje-rod da Faransa tun da fari, wannan shi ne karon farko da ake cire kasar da ta lashe kofi da wadda ta zo ta biyu a gasar baya a zagayen farko na wata sabuwar gasar ta cin kofin duniya.

Slovakia zata kara da kasar Netherlands a zagaye na biyu na wannan gasa ranar litinin. 'Yan wasan Netherlands sun doke 'yan kasar Kamaru da ci 2 da 1 a Cape town a wasan da bai shafi matsayin kowace kasa a wannan rukuni nasu ba. Netherlands ta lashe dukkan wasanni ukun da ta buga a zagayen farko, ta samu maki 9 inda ta zo ta daya a rukuni na 5 ko "E".

Paraguay ta yi kunnen-doki babu kare bin damo da New Zealand a Polokwane, amma duk da wannan ita ce ta lashe rukuni na 6 ko "F" ta kuma tsallake zuwa zagaye na biyu. Paraguay ta samu maki 5, kuma zata haye zuwa zagaye na biyu a karo na hudu cikin tarihin kasar. New Zealand ta kammala wasan zagayen farko da maki 3, amma duk da haka 'yan wasanta zasu koma gida. Italiya ce kashin baya a wannan rukuni.

Japan ta doke Denmark da ci 3 da 1 a Rustenberg, ta zo ta biyu a bayan bayan Netherlands a rukuni na biyar ko "E". Ita ma zata haye zuwa zagaye na biyu inda a ranar talata zata kara da kasar Paraguay.

XS
SM
MD
LG