Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zaben APC a Bauci da Gombe


APC
APC

​A Najeriya babbar jam'iyyar adawa APC ta gudanar da zabubbuka a wassu jihohi don fidda shugabannin ta.

Wannan rukunin zabe da aka gudanar a karshen mako shine zangon karshe a shirye-shirye da jam'iyyar keyi domin tunkarar zaben 2015 idan Allah Ya kaimu.

A jihar Gombe misali, jagoran jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Senata Muhammad Danjuma Goje shine ya yaye kallabin shirin gudanar da zaben.

Wani jigo a jam’iyyar, kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar tarayya, Usman Bayero Nafada, yayi tsokaci akan karbuwar jam’iyyar a jihar Gombe.

“Abinda muka gani, zaku iya bada labarin cewa canji, kamar yazone a jihar Gombe, illa dai ana jiran lokaci,” inji Mr. Nafada.
Majidadin Gombe, Injiniya Sa’adu Abubakar Abdullahi, jigo ne a jam’iyyar amma ya kauracewa zaben. Ko meyasa?

“Dalilinmu dai shine, shinfidin zaben wato shugabancin kasa ba’a yi shi ba tukunna, kaga idan mun shiga, kamar mun yi amai ne mun kwashe,” Mr. Sa’adu Abubakar kennan yake mayar da martani.

To sai dai kuma a jihar Bauci, an samu rudani wajen gudanar da zaben, saboda karar da wasu ‘yan jam’iyyar suka shigar kotu domin ta tsayar da zaben. Daga bisani dai an gudanar da zaben cikin dare, zuwa wayewar Lahadinnan. Yanzu haka ana jiran sakamakon zaben.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG