Accessibility links

Rahotanni daag Jihar River da ke Kudu maso kudancin Najeriya na cewa, har yanzu wasu kungiyoyi fararen hula, na ci gaba da gudanar da zanga zanga domin neman a soke zaben jahar da aka gudanar a kwanan nan.

Wakilin Muryar Amurka Sanusi Lamido ya kara da cewa ko a baya bayan nan an samu kungigoyin kasa da kasa da suka gudanar da taruka na neman a soke zaben domin irin magudin da suka ce an tafka.

Sun kuma yi zargin cewa an tursasa mutane wajen yin zabe kana an razana wasu da dama ta hanyar harbe-harben bindiga a lokacin zaben.

Zaben na Jahar Rivers ana takaddama ne tsakanin dan takarar PDP Nyesom Wike da Dakuku Peterside na jam’iyar adawa ta APC.

A baya bayan nan ‘yan jam’iyyar ta APC suka gudanar da zanga zanga a ranar juma’ar da ta gabata a gaban ofishin hukumar zabe ta INEC bayan da hukumar zaben ta yi jinkiran bin umarnin kotu.

A kwanan ne kotun sauraren korafe-korafen zabe ta nemi hukumar at INEC da ta mika mata takardunzaben jihar.

A daya bangaren kuma, hukumar ta INEC ta ayyana cewa a ranar 23 na wannan wata za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jahar.

Ga karin bayani daga wakilinmu Sanusi Lamido a tattaunawarsu da Halima Djimrou:

XS
SM
MD
LG