Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Khan, Musulmi Na Farko, Magajin Garin Birnin Landan.


Sadiq khan, sabon magajin garin birnin Landan.
Sadiq khan, sabon magajin garin birnin Landan.

Wannan ya nuna sakewar lokaci da yanayi ga Britaniya da al-umar musumin kasar su kamar milyan 3.

A Ingila an zabi Sadiq khan, musulmi na farko; magajin garin birnin Landan, a wani mataki da ake gani na sauyin lokaci ga Ingila, da kuma musulman da suke kasar, su kusan milyan uku.

"Shi musumi ne. Mu musulmai ne. Wannan babbar dama ce ga al'umar musulmi," inji wani dan kasuwa mai suna Mohammed dan shekaru 69 da haifuwa, wanda yake gabashin birnin Landan, unguwar da galibin jamar dake wurin musulmi ne.

Shekaru fiyeda 50 ne, dan kasuwan Mohammed, ya kaura zuwa Ingila, a lokacinda ake nunawa musulmi wariya.

Nasarar da Sadiq khan ya samu, alamace ta canji daga abunda aka sani a baya a kasar. A cikin shekaru 60 da suka wuce, birnin Landan ya sake daga zama wuri indi jinzi daya yake, zuwa birni mai yawan al'adu, da mutane daban daban daga sassan duniya.

Amma sakamakon sauran zabe a duk fadin kasar, ya nuna rarrabuwar kawuna tsakanin sauran jama'ar kasar, musamman kan batun bakin haure.

Rahotanni sun nuna cewa in banda a birni Landan din,inda Khan na jam'iyyar Labor ya sami nasara da kuma a wasu wurare kalilan, jam'iyyar ta Labor ta sha mummunan kaye rabon data ga haka fiyeda shekaru dari.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG