Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Anfani Da Addini Domin Yaudarar Jamaa’a a Najeriya


Obama
Obama

Ban san abinda yasa a Najeriya wannan zarbewan ya zama haka ba,domin abinda yasa nace zarbewan yayi yawa shine, a Najeriya anfi yin maganar addini fiye da nan Amurka ba wai babu masu addini anan ba, akwai musulmai akwai kirista.

Farfesa Samuel Zalanga malami a jamiaar dake jihar Minosota ne ke wannan kalamin lokacin da suke tattaunawa da Grace Alheri Abdu, game da yadda ake anfani da addini wajen neman mukami ko wata alfarma a Najeriya, sabanin abinda ke faruwa anan Amurka.

Farfesan ko yana sharhi ne akan jawabin da shugaba Obama yayi wa Amurkawa na shekara-shekara domin bayyana halin da kasa take cikin wanda kuma wannan jawabin shine irinsa na karshe da shugaban yayi wa ‘yan kasar.

Shugaban ya tabo batutuwa da dama ciki ko harda cewa Amurkawa tsintsiya ce madaurin ki daya ba tare wani banbancin kala, addini ko siyasa ba muddin aka zo batun gina kasa.

Farfesa Zalanga yace ba zaka zagaya unguwa kaga mujamia ko masallaci ba, kuma ba wai ba a addini bane anan.yace amma labarin yasha ban-ban .

Farfesan yace kafin zuwan sa Amurka yayi aiki a Bauci akwai masallatai da mujamiu a ciki garin tun a wancan lokacin yanzu ma adadin ya karu, amma wuraren ibada ne kawai ba tsoron ALLAH a zukatan jama’a.

Yace a Najeriya addini ne yakamata ta kawo canjin zuciya da tsoron ALLAH domin kar kaje kaci kayan wani kaci hakkin wani abinda ba naka ba, amma sai asabanin haka kake gani.

Farfesa ya bada musali da gwamnan jihar Illinois da yaso ya karbi na goro domin maye gurbin Shugaba Obama lokacin da ya zama shugaban kasa, yau yana kulle gidan yari.

Yace a Najeriya sai shugabanni suje coci ko masallaci suyi maganar ALLAH amma suna sahun gaba wajen cutar mutane, amma kuma mutane basu damuwa su tambayi me yasa suke haka.

Farfesa Zalanga yace akwai maganar ALLAH da yawa wajen ‘Yan Najeriya amma kuma babu tsoron Allah wajen cin hakkin jamaa, abubuwan da ake rubutawa a jaritui abin ya zama kazanta, a Najeriya zaka ga wani zai mutu akan dubu 3 amma kuma ga wani can ya kwashe miliyoyin kudi shi kadai.

Yace idan ka taba irin wannan mutum din sai kaji yace maka shi mai tsoron ALLAH ne, su sa manyan kaya kuma suna son mu basu girma amma ba girman da zasu yi anfani dashi domin kyautata rayuwar dan Adam ba.

Ga Grace da ci gaban hirar tasu

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:47 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG