Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zaben Kasar Togo


Faure Gnassingbe
Faure Gnassingbe

Daga jiya asabar ne aka bude rumfunan zaben shugaban kasar Togo. Shugaban kasar mai ci a yanzu Faure Gnassingbe na neman tazarcen karo na uku wanda in ya samu zai zama iyalan gidansu ke mulkar kasar shekaru kusan hamsin.

Masu sa ido a zaben kasar Togo sun ce mutane masu yin zabe sun fito da kimanin kaso arba'in na masu kada kuri’ar. Faure Gnassingbe ya dare karagar mulki a shekarar 2005 bayan mutuwar mahaifinsa Gnassingbe ​Eyadema wanda ya mulki kasar tsawon shekaru talatin da takwas.

Shima Jean-Pierre Fabre da ya taba fitowa takara a zaben da ya gabata ana sa ran zai zo na biyu a zaben tashin farko na zaben shugaban kasa.

Masu rajin kare hakki sun soki Togo da amfani da karfin tuwo akan masu zanga-zanga. Daruruwan masu sa ido sun sauka a Togo don ganewa idanunsu yadda zata kaya a zaben da ake sa ran masu kada kuri’a Miliyan 3 da rabi ne da zasu wakilcin rabin yawan jama’ar kasar.

XS
SM
MD
LG