Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Cigiyar Amurkawan Da Aka Sace A Gabar Tekun Najeriya


Jirgin ruwa a cikin teku
Jirgin ruwa a cikin teku

'Yan fashi da makami kan teku da suka sace Amurkawa biyu ana nemansu ruwa a jallo.

Mahukuntan Najeriya suna cigaba da cigiyar Amurkawa biyu da wasu 'yan fashi da makami suka sace kan ruwan tekun kasar.

Matukin jirgin da inginia nashi aka sace yayin da suke tuka wani jirgin ruwa mai jigilar danyan man fetur mai dauke da tutar Amurka ranar Laraba cikin sashin ruwan kasa da kasa gap da daurar Najeriya.

Jirgin mallakar wani kamfanin Amurka ne mai suna Edison Chouest Offshore. To sai dai kawo yanzu kamfanin bai ce uffan ba kan lamarin

Jami'an Amurka sun ce barayin sun saki jirgin da sauran ma'aikatan ba tare da cire ko kwandala ba daga jirgin. Ba'a sani ba ko Amurkawan har yanzu suna wani wuri cikin tekun ko kuma an kaisu cikin wani sunkuru.

Sojojin Najeriya sun bada umurnin a soma cigiya cikin gaggawa domin a ceto mutanen biyu. To sai dai jami'an gwamnatin Najeriya sun ki su tabbatar ko wasu dakarun sojin Amurka sun shiga cigiyar.

Jami'an tsaron Amurka sun ce suna bin lamarin domin sansanin sojin Amurka mafi kusa shi ne na sojojin kuntunbala dake Mashigin Tekun Guinea.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Marie Harf ta ce Amurka ta damu game da lafiyar 'yan kasarta biyu da aka sace. Ta kara da cewa Amurka na neman yadda za'a warware lamarin cikin lumana.

Harf ta kuma nuna damuwa da yawan karuwar 'yan fashi da makami kan Mashigin Tekun Guinea. An samu karuwar fashi da makami a wannan yankin duk da raguwar irin wannan aika aikar a wasu wurare a duniya.

Hukumar Kula Da Zirga zirgan Jiragen Ruwa Ta Kasa Da Kasa ta ce a rabin wannan shekarar 2013 kawai an samu aukuwar irin wannan mugun abu sau talatin da daya.
XS
SM
MD
LG