Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Bayyana Ra'ayoyi Da Yin Bayanai Kan Ranar Dimokaradiyyar Nijeriya


Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

A yayin da ake shirin shagulgulan ranar dimokaradiyya a goba 29 ga watan Mayu, 'yan Nijeriya na ta bayyana ra'ayoyinsu game da halin da kasar ke ciki; ita kuma hukuma na ta bayani.

'Yan sa'o'i kafin a fara shagulgulan zagayowar ranar dimokaradiyyar Nijeriya, 'yan kasar na ta bayyana ra'ayoyinsu game da halin da ake ciki a kasar; a yayin da su kuma jami'an gwamnati ke ta bayani.

Wakilinmu a birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, Nasiru Elhekaya, ya aiko ma na da rahoton cewa a Nijeriya, wadda akasarin jama'arta sun fi dogara ne kan wutar lantarki, abin da gwamnati ta fi alkawarin gyarawa ita ce wutar lantarki. Nasiru ya ruwaito karamin Ministan Kudi Yarima Ingawa na bayyana cewa kwanan nan kararrakin janaretocin wuta za su zama tahiri a Nijeriya. Ya ce tuni aka girke wani dirkeken injin din wutar lantarki a Kokin Gurara, wanda zai samar wa Kaduna wuta sannan daga nan kuma ya yada wutar zuwa sauran jihohin kusa.

Shi ko Alhaji Muhammadu Magaji, Sakataren Yada Labaran Kungiyar Manoman Nijeriya, ya ce tsarin da ake bi wajen rabon taki ya fi na gabanin lokacin dimokaradiyya; yayin da shi kuma wani mazaunin arewa maso gabashin Nijeriya mai suna Sabo Imamu Gashuwa ke cewa ana ta daukar kudaden da ya kamata a yi amfani da su wajen ayyukan cigaba ana ta bararwa da sunan matakan tsaro. Su kuma nakasassun Nijeriya sun yi barazana ce cewa nan gaba ba su ba wanda ya ki tafiya da su. Alal misali, wani nakasasshe mai suna Aminu Tudun Wada ya ce nan gaba za su mara baya ne ga duk wanda ya ba su Mataimakin Shugaban Kasa ko kuma Mataimakin Gwamna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG