Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana farautar wani mutum daya kashe mutane a Faransa

Mutane a inda aka kashe wasu a Faransa.
Mutane a inda aka kashe wasu a Faransa.

Hukumomin kasar Faransa sun kaddamar da farautar mutumin da ake kyautata zaton ya maida karkashe mutane sana’a, wanda ya bude wuta a wata makarantar Yahudawa a birnin Toulouse dake yammacin kasar, ya kashe wani limamin Yahudawa da ya yansa biyu da kuma ‘yar shugaban makarantar.

Wannan ne mumunar harbi na uku da aka yi a yankin Toulouse cikin kwanaki takwas da wani dan bindiga akan babur yake amfani da makami iri daya. A al’amurra guda biyu na farko maharin ya bude wuta ya bude wuta ne akan sojojin Faransa ya kashe uku daga cikinsu.

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, maza maza yaje makarantar da aka kaiwa hari, yace yayi imanin cewa hare haren guda uku suna da alaka da nunawa tsirarun kasar bambamci. Nan da nan kuma hukumomi suka dauki tsauraran matakan tsaro a makarantun Yahudawa da Musulmi da kuma wuraren ibada a yankin.

Shedun gani da ido sunce dan bindigan wanda ya rufe fuskarsa da hular kwano, da sanyin safiya, ya kutsa makarantar kafin a fara karatu ya bude wuta akan limamin Yahudawa da yara uku, dukkansu babu wanda ya kai shekara goma da haihuwa. Haka kuma an harbi wani saurayi dan shekara goma sha bakwai wanda yaji mumunar rauni.

XS
SM
MD
LG