Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Murnar Sako Dr. Shettima Ali Monguno


'Yan makaranta su na shigewa dab da wani masallaci a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno
'Yan makaranta su na shigewa dab da wani masallaci a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno

Daruruwan mutane, manya da kanana, su na ci gaba da zuwa gidan Dr. Shettima Ali Monguno, domin nuna farin cikin sako shi da aka yi.

Dubban mutane su na tururuwa zuwa gidan tsohon ministan albarkatun man fetur, Dr. Shettima Ali Monguno, domin taya shi da iyalansa murnar sako shi da aka yi, bayan da ya shafe kwanaki uku a hannun wasu 'yan bindiga.

Wakilin Muryar Amurka a Maiduguri, Haruna Dauda, yace yau litinin da rana ne labari ya bazu a cikin Maiduguri cewa an sako Dr. Monguno, kuma ya komo gida. Hukumomi sun ce an sako shi a yankin Marte, ya kuma komo gida tare da direbansa,

Wakilin namu ya ce ya ga Dr. Monguno cikin koshin lafiya, sai dai alamar gajiya da ya gani a jikinsa kawai. Dr. Monguno bai yi magana ba, amma iyalinsa sun nuna farin ciki tare da godiyar sako shin da aka yi.

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya bayyana cewa ba a biya ko sisin kwabo domin sako dattijon ba. yace wadanda suka sace shi, su ne suka sako shi domin radin kansu, musamman a bayan rokon da jama'a suka yi.

Ga rahoton na Haruna Dauda daga Maiduguri:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG