Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Gwamna Nyako Da Yiwa Shugaba Jonathan Shishshigi


Shugaba Jonathan da tsohon shugaban PDP Bamanga Tukur da suka bata da Gwamna Murtala Nyako
Shugaba Jonathan da tsohon shugaban PDP Bamanga Tukur da suka bata da Gwamna Murtala Nyako

Kungiyar masu ruwa da tsaki ta jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ta zargi gwamnan jihar da yiwa mulkin shugaba Jonathan shishshigi

Ana cikin yunkurin da majalisar dokokin jihar Adamawa keyi na tsige gwamnan jihar Murtala Nyako sai gashi kungiyar masu ruwa da tsakin PDP ta Adamawa ta dorawa gwamnan jihar laifin furta wasu kalamun da basu da dadi ko gaskiya.

Kungiyar ta nuna bacin ranta da abun da ta kira shishshigin da gwamnan keyi akan mulkin shugaba Jonathan yayin taronta a Abuja. Tace hakan bai taimaka wurin dawo da zaman lafiya ba a jihar.

Tsohon kantoman jihar Filato Aircommodore Dan Suleiman shi ne shugaban taron da aka gudanar a Abuja. Yace basu yadda da maganar da gwamnan yayi ba domin maganar bata da kyau. Misali, gwamnan yace tashin hankalin da 'yan Boko Haram keyi a arewa maso gabas, wai Jonathan ne ke haddasa shi da sojojin kasar.

Shugaban kungiyar ya kira gwamnan ya gyara zamansa. Rashin juttuwa da shugabannin PDP yasa gwamnan ya canza sheka zuwa APC.

Dangane da zaben 2015 Dan Suleiman yace babu shakka suna son PDP ta kwace mulkin jihar a zabe mai zuwa.

A gefe guda kuma jam'iyyar APC ta nuna damuwa da abun da take gani bita da kulli ne ga nasarar adawa akan gwamnati mai ci. Mai Mala Buni sakataren APC na jihar Adamawa yace shure-shure ba ya hana mutuwa. Gwamnatin Najeriya tana barin ana yiwa mulkin dimokradiya karan tsaye.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG