Accessibility links

Ebola Tayi Kamari a Saliyo

  • Jummai Ali

Wani malami yana auna zafin jikin dalibai.

Wani malami yana auna zafin jikin dalibai.

Sabbin kididdiga da aka yi sun nuna cewa bular anobar zazzabin Ebola tana yin kamari a kasar Saliyo, duk da cewa ana samu raguwar anobar cutar a wasu kasashen Afrika ta yamma.

Bayanai na nuni da cewa bular anobar zazzabin Ebola tayi kamari a kasar Saliyo, duk da cewa ta sassauto a wasu kasashen Afrika ta yamma.

Kungiyar Lafiya ta duniya tace kasar Saliyo ta tabbatar cewa a karshen watan jiya na Nuwamba, mutane 537 aka tabbata sun kamu da cutar a kasar, karin fiye da mutane 150 ke nan cikin mako guda.

Bayani na baya bayan da aka gabatar Laraban nan, kungiyar Lafiya ta Duniya tace anobar tafi kamari a birnin Freetown inda aka bada rahoton fiye da mutane maitan sun harbu da kwayar cutar.

Kungiyar tayi bayani cewa fiye da mutane dubu 17 ne suka kamu da cutar a duk fadin duniya, Kuma ya zuwa yanzu cutar ta kashe kimamin mutane dubu 6 da 70.

Rahoton na kungiyar lafiya ta duniya yace an samu sasautowar bular anobar a kasar Guinea wadda ta bada rahoton cewa mutane 77 suka kamu da cutar a makon jiya. Kasar Liberia kuma ta bada rahoton cewa mutane 43 ne suka kamu da cutar.

XS
SM
MD
LG