Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Sha Alwashin Kalubalantar PDP


APC
APC

Gwamnan Adamawa Murtala Nyako a wani taron jam'iyyar APC ya nuna bacin rai kan abun da ya KIRA kuntatawa 'ya'yan jam'iyyar APC a jihohin dake karkashin mulkin PDP

Yayin taron da APC ta yi gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya kira gwamnatin tarayya ta yi masu sassauci daga masifun da ya yi zargin ita gwamnati tarayya ke haddasa masu. Ya nuna bacin ransa kan yadda gwamnatin tarayya ke kuntatawa 'yan jam'iyyarsa musamman a jihar Rivers inda ko a kwanan nan aka harbi Sanato Abe da mai taimakawa gwamna Amaechi.

Jam'iyyar ta kara da cewa ana musguna masu a kokarinsu na bude ofisoshi a jihohin dake karkashin ikon PDP. Tsohon kakakin majalisar wakilai Alhaji Aminu Masari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa ya ce maganar Rivers bata APC kadai ba ce. Magana ce da ta shafi kasar gaba daya domin yadda ake karya doka da cin zarafin mutane. A jihar ne 'yansandan Najeriya suka zama 'yansandan PDP. Ya ce zasu dauki duk matakan da suka dace su kawo gyara. Ya ce zasu kare dimokradiya da mutuncin 'yan jam'iyyarsu koina a Najeriya cikin matakin bin doka da oda da yin anfani da abun da doka ta tanada.

Dan majalisar wakilai Kawu Sumaila na ganin jam'iyyar APC ta kama hanyar karbe madafin iko daga PDP ta lashe zaben shekarar 2015. Ya ce idan da karantwa ake yi yanzu mutane sun gani sun kuma ji a jikinsu. Dole yanzu canji suke so, canji kuma a koina.

APC ta yi alkawarin magance rikicin cikin gida a Kano da Sokoto kuma zata fara yin ragistan sabbin 'yan jam'iyyar a watan gobe. Sanato Kabiru Gaya ya kara haske ya ce Dr Musa Kwankwaso shi ne shugaban APC a Kano kuma ya kamata Ibrahim Shekarau ya hakura domin a samu cigaba.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG