Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Archbishop Desmond Tutu ya cika shekaru 80 da haihuwa

Archbishop Emeritus Desmond Tutu.
Archbishop Emeritus Desmond Tutu.

Membobin Ikilisiya, da ‘yan siyasa har ma da shahararrun mawaka sun taru a babbar majami’ar St. George mai tarin tarihi ta birnin Cape Town, domin bukin tunawa da cika shekaru 80 na Achbishop Desmond Tutu.

Daruruwan mutane suka taru a majami’ar da Archbishop Tutu ya taba yin jawabin kin jinin wariyar launin fata.

Mawakin nan Bono na kungiyar U2 ya raira wakar yaba rayuwar Archbishop Tutu wanda ya bayyana a matsayin mafi shahara a cikin taron.

Matar Nelson Mandela Graca Machel da mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Kgelema Motlanthe suna daga cikin manyan bakin da suka halarci bukin.

Archbishop Tutu ya godewa Motlanthe domin halartar bukin duk da matsalolin da aka fuskanta.

Farkon wannan makon Archbishop Tutu ya kushewa gwamnatin shugaba Jocob Zuma domin hana Dalai Lama takardar izinin shiga kasar, wanda yake cikin jerin wadanda aka gayyata bukin. Archbishop Tutu yace gwamnatin Mr. Zuma tafi tsohuwar gwamnatin wariyar launin fata muni.

XS
SM
MD
LG