Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asarar Da Makiyaya Suka Tafka Sakamakon Ta’addancin Boko Haram


Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.
Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.

Hadakar kungiyar kare hakkin makiyaya ta Najeriya, Weti Welli ta koka da cewa sama da makiyaya 380, suka rasa rayukansu baya kuma ga sama da shanu dubu 17, sakamakon rikicin Boko Haram a jihar Adamawa kawai, batun da kungiyar tace ya kamata gwamnati ta duba lamarin.

A wajen taron gangami da kungiyar ta gudanar a Yola, shugabannin kungiyar sun yi zargin cewa ana nuna musu shakulatin bangaro game da halin da makiyaya da rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya.

Shugaban kungiyar Alhaji Alkali Bello Madagali, ya bayyana halin da suka shiga inda yace cikin shekaru ukun da suka gabata ‘yan Boko Haram sunyi musu barna sosai, har ma ya nemi taikamon gwamnatin jiha da ta Tarayya da sauran kungiyoyi.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar makiyaya a jihar Adamawa Hon Jibrin Hamankeri, ya nemi gwamnati da ta taimakawa ko da daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da abin ya shafa.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG