Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun yaki da kanjamau, zazzabin cizon sauro da tarin fuka ya sami tallafi


Bill Gates
Bill Gates

Asusun yaki da cutar kanjamau da zazzabin malariya da kuma tarin fuka na duniya da ya taimaka wajen ceto rayukan miliyoyin mutane, ya sami tallafin dala miliyan dari bakwai da hamsin domin ci gaba da gudanar da ayyukanshi.

Asusun yaki da cutar kanjamau da zazzabin malariya da kuma tarin fuka na duniya da ya taimaka wajen ceto rayukan miliyoyin mutane, ya sami tallafin dala miliyan dari bakwai da hamsin domin ci gaba da gudanar da ayyukanshi.

Asusun tallafi na Bill da Milinda Gates ya sake bayyana niyar tallafawa asusun na duniya yau ne, a wajen wani taron tattalin arziki na duniya da aka saba gudanarwa shekara- shekara wanda aka yi a Davos, Switzerland.

An kafa asusun na duniya ne shekaru goma da suka shige ana kuma amfani da shi wajen taimakawa ‘yan kasa, da masu ilimin kimiyya da gwamnatoci wajen gano sababbin hanyoyi da dabarun yaki da cututukan.

Asusun na duniya yace matakan da ya dauka sun taimaka wajen ceton rayukan sama da mutane miliyan shida da dubu dari biyar a duniya. Ya kuma yi kiyasin cewa, shirin da yake marawa baya zai ceci sama da wadansu rayuka miliyan daya cikin shekarar nan.

Bisa ga cewar asusun kimanin rabin wadanda ke dauke da cutar kanjamau da ke shan magani a kasashe marasa karfin tattallin arziki, suna samun tallafi daga asusun. Asusun ya kuma bayyana cewa ana samun kimanin kashi tamanin da biyar bisa dari na maganin zazzabin cizon sauro da kuma kimanin kashi tamanin bisa dari na maganin tarin fuka, daga cibiyoyin da asusun ke tallafawa.

Cibiyoyin lafiya na duniya sun ce wadanda suka fi fama da cutar kanjamau da zazzabin cizon sauro suna kasashen Afrika yankin kudancin Sahara. Nahiyar kuma tana daya daga cikin kasashen da aka fi samun yawan mace mace ta dalilin kamuwa da tarin fuka.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG