Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba A Bukatar Yin Rigakafin Shawara Sau Biyu


Ana bada rigakafin shawara
Ana bada rigakafin shawara

Hukumar lafiya ta duniya tace ba a bukatar yiwa mutum karin rigakafin cutar shawara karo na biyu bayan shekaru goma kamar yadda aka saba.

Hukumar lafiya ta duniya tace ba a bukatar yiwa mutum karin rigakafin cutar shawara karo na biyu bayan shekaru goma kamar yadda aka saba. Kwararru sun bayyana cewa allurar rigakafi da aka yiwa mutum sau daya ta isa ta kare shi daga kamuwa daga cutar ta shawara duk tsawon rayuwarshi.

Wannan sanwarwar ta biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, tunda aka fara yin allurar rigakafin a shekara ta 1930, mutane 12 kadai aka samu da suka kamu da cutar bayan an yi masu allurar rigakafi bayan yiwa kimanin mutane miliyan dari shida rigakafi.

Hukumar ta bayyana cewa, sanin wannan yana da muhimmanci ga matafiya da kuma kasashen da ake fama da cutar.

An kiyasta cewa kimanin mutane dubu dari biyu ne suke kamuwa da cutar yellow fever kowacce shekara. Kimanin kashi 15% na wadanda suka kamu da cutar shawara, suna fama da zazzabi mai tsanani da ciwon mutuwar gababuwa da zubar jini, kuma yawancin mutanen suna mutuwa domin ciwon shawara bashi da magani.

Allurar rigakafi ita ce kadai hanyar da tafi amfani wajen shawo kai da maganin ciwon shawara, kashi casa'in cikin dari na mutanen da aka yiwa rigakafin shawara suna samun kariya cikin kwanaki 30 da yin rifakafi.

Ciwon shawara cura ce da sauro ke yadawa, kuma ana fama da cutar a kasashe 44 na nahiyar Afirka.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG