Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Kafa Dokar Hana Fita Sabuwa a Maiduguri ba


Sojoji masu yin sintiri a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Sojoji masu yin sintiri a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Zanna Umar Mustapha, yace umurnin da aka bayar na shiga gida daga karfe 6 na maraice, na jiya jumma'a ce kawai.

Mataimakin gwamnan Jihar Borno yace hukumomin tsaro sun bukaci jama'a su shiga gidajensu daga karfe 6 na maraice a jiya jumma'a ne kawai domin su samu sukunin bin sawun tsagera 'yan bindigar da suka buya a wasu sassan birnin, a bayan da aka fatattake su daga barikin Giwa.

Yace tun daga yau asabar, kowa yana iya fita yaje harkarsa har zuwa karfe 9 na dare, lokacin da aka saba komawa gidaje har zuwa karfe 6 na asuba.

Mataimakin gwamnan ya roki jama'ar Maiduguri da na Borno da su bayar da cikakken hadin kai ga sojoji da sauran jami'an tsaro da ma yaran nan da ake kira "yan Gora ko Civilian JTF, ta hanyar tsayawa da bin umurnin jami'an tsaro a duk inda ake gudanar da aikin binciken mutane da ababen hawa.

Alhaji Zanna Umar Mustapha ya bayyana hamdala cewar sojoji da jama'a sun samu nasara a kan 'yan bindigar da suka kai hari, yana mai cewa da safiyar yau asabar ma sojojin sun bi sawu tare da kai farmaki a kan wasu daga cikin tsageran da suka kubuta suka yi kokarin gudu su bar gari.

Yace da ikon Allah an fara ganin karshen wadannan tsagera ke nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG