Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Duk Ministoci 36 Ne Zasu Samu Mayan Ofisoshi Ba


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu, Buhari, ya ce ba duk Ministoci 36, ne zasu samu mayan ofisoshi kamar yada yake a can baya ba.

Wannan kalamai dai ya jawo kace nace tsakanin al’umar kasa a yadda wasu ke zargin Gwamnatin Muhammadu Buhari, da nuna gazawa tun kafin tafiya tayi nisa, a yadda wasu kuma ke ganin matakin shugaba Buhari, zai taimakawa kasar wajen rage makudan kudaden da ake kashewa akan manyan jami’an Gwamnati masu rike das mukaman siyasa irin na Ministoci.

Matakin na Muhammadu Buhari dai ana ganin tafkar Gwamnati ce da zata tafi da Minstoci irin na jeka nayika.

Pastor Tunde Bakare, wanda ya taba zama mataimakin dan takarar neman shugaban kasa na jami’iyyar CPC tare da Muhammadu Buhari, ya kare matakin shugaban kasan inda yake cewa matakin da ya dauka na tafiya da wasu ‘yan siyasa da wasu ke zargi, cewa tsofaffin zuma ne abun yabawa ne kuma dole ne shugaban kasan ya tafi da wadanda ya sani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG