Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Yi Alkawarin Kwato 'Yan Matan Chibok Ba- Buhari


Janar Buhari sabon shugaban Najeriya mai jiran gado
Janar Buhari sabon shugaban Najeriya mai jiran gado

Yayin da ake bikin tunawa da cika shekara guda da mayakan Boko Haram su ka sace 'yan matan Chibok, zababben shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce, ba za su yi alkwarin kubutar da 'yan matan ba, amma za su dauki matakan da suka fi na gwamnati mai ci.

Zababben shugaban kasar Najeriya Janar Muhammadu Buhari, ya ce ba zai yi alkawarin cewa gwamnatin sa tana da tabbacin samo ‘yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace guda 219 a garin Chibok dake arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta wuce ba.

A cikin wani bayani da ya yi jiya Talata, lokacin da aka cika shekara ‘daya da sace ‘yan matan Chibok, ya ce, “bamu sani ba ko za’a iya ceto ‘yan matan Chibok.”

Janar Buhari ya kalubalanci gwamnati mai ci a yanzu da rashin kokarin neman ‘yan matan, ya na mai cewa “gwamnatin sa ba za ta yi abin da wannan gwamnatin ta yi ba”. ya kuma kara da cewa, a ranar da ya karbi ofis idan Allah ya yadda, kungiyar “Boko Haram za ta san iyakacin karfin mu.”

Kungiyar kare rajin ‘dan Adam ta duniya, Amnesty Internationl, ta ce mayakan Boko Haram sun sace mata a kalla dubu biyu a Najeriya, tun farkon shekarar ta 2014, tana kuma tilastawa yawancin matan wajen keta musu hadi, da maida wasu mayakanta.

XS
SM
MD
LG