Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Shugaban Addinin Iran Ya Wancakalar Da Zargin Amurka


Babban shugaban Addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei , ya na jawabi a ranar Asabar 15 ga watan oktoba a lardin Kermanshah a yammacin kasar Iran.
Babban shugaban Addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei , ya na jawabi a ranar Asabar 15 ga watan oktoba a lardin Kermanshah a yammacin kasar Iran.

Ayatollah Ali Khamenei ya ce ikirarin Amurka ba shi da kan gado kuma zargin da ta ke yi ba shi da tushe

Babban shugaban addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khameini ya ce ikirarin da Amurka ke yi cewa gwamnatin kasar Iran ta tallafawa makarkashiyar neman kashe jakadan Saudiyya , ikirari ne marar kan gado.

Babban shugaban addinin ya zargi Amurka da yin zargin da ba tushe a kan ‘yan kasar Iran kalilan da ke Amurka da zama, duk don ta maida Iran saniyar ware.

Sakataren shari'ar kasar Amurka, Eric Holder, ya ke kara jaddada zargin na Amurka da kuma irin matakin da aka dauka akan wadanda ake zargi da kitsa makircin.
Sakataren shari'ar kasar Amurka, Eric Holder, ya ke kara jaddada zargin na Amurka da kuma irin matakin da aka dauka akan wadanda ake zargi da kitsa makircin.

Ya yi wannan furuci ne a yau asabar a jawabin da ya yi a lardin Kermanshah. An nuna jawabin a talbijin din gwamnatin kasar.

Ranar talatar da ta gabata ma’aikatar shari’ar Amurka ta yi sanarwar cewa ta wargaza wani shirin kasar Iran na neman yin kisan gilla ga jakadan Saudiyya na nan Amurka, Adelal Jubeir. Jami’ai sun ce Amurka ta shigar da kara a kan wasu Iraniyawa biyu bisa zargin su da hannu a cikin shirin. Jami’an sun ce daya daga cikin mutanen biyun da ake zargi mai suna Gholam Shakuri ya yi zama a cikin rundunar tsaron juyin juya halin kasar ta Iran.

Furucin da shugaban addinin kasar Iran ya yi a yau asabar shi ne martanin farkon da ya maida kai tsaye game da ikirarin na Amurka, duk da cewa kananan jami’an kasar ta Iran sun musanta zargin a farkon makon nan.

A jiya Jumma’a mai magana da yawun ma’aikatar shari’ar Amurka, Victoria Nuland ta ce a wannan mako gwamnatin Amurka ta yi ganawar kai tsaye da jami’an gwamnatin kasar Iran akan maganar makarkashiyar neman yin kisan kan da ake zargin an shirya.

Ta gayawa manema labarai cewa an yi ganawar ce domin a fada kiri-kiri, a bayyane cewa Amurka ba za ta lamunta da irin wannan halayya da take-take ba , kuma irin haka ya sabawa ka’idojin Amurka da na kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG