Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Magudanar Ruwa a Kasuwar 'Yan Lemu Dake Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Bayan an kwashe fiye da shekaru talatin ana hada hadar kasuwancin kayan marmari irin su lemu da sauransu har yanzu kasuwar bata da magudanar ruwa ko isasshen wurin ajiye manyan motoci dake jigilar kaya.

Kasuwar lemu dake Kano ta fi shekara talatin da aka kafata inda ake cinikayya akan kayan marmari kamar su lemu, gwanda ayaba, kankana, abarba, mangwaro da dai ire-irensu.

'Yan kasuwa daga kudanci da arewacin kasar Najeriya da kasashe dake makwaftaka da Najeriya suke saye da sayarwa a kasuwar.

Sakataren kungiyar masu sayarda kayan marmari ta Najeriya reshen jihar Kano Ismaila Saidu Koki yace kamar abarba sukan samu motoci kusan arba'in kullum.Mutane daga jihohi daban daban suke zuwa sayen kayan. Ita kuwa kankana idan ta kama sukan sauke motoci hamsin a rana guda. Mutane daga Legas ko Fatakwal suna zuwa su yi lodin kayan marmarin daga kasuwar. A kullum ana harkar nera miliyan hamsin.

Wani Obi Maikwakwa yana cikin masu kawo kaya daga birnin Legas. Shi yana kawo kwakwa ne cikin tireloli daga Legas. Yayi kimanin shekara goma sha biyar yana kawo kwakwa Kano. Yace a wata guda sukan kawo tireloli kusan talatin.

Shi ma Joseph daga jihar Binuwai yace yana kawo kaya daga Katsina-Ala kuma ya kwashe shekaru da dama yana kawo kayan.

Ahmed Yusuf Ibrahim daya daga cikin masu sayen kaya daga hannun fatake su sayarwa kananan 'yan kasuwa. Yace idan sun bude mota suna ba wadanda zasu shiga gari su sayar . Bisa ga ka'ida sukan basu kwana biyu ko uku kafin su kawo kudinsu.

Duk da rawar da kasuwar ke takawa wurin habaka tattalin arzikin jama'a daban daban sakataren 'yan kasuwan Ismaila Saidu Koki yace akwai kalubale da suke fuskanta. Abun da ya fi ci masu tuwo a kwarya shi ne rashin magudanar ruwa da kuma isasshen wurin ajiye motoci. Yanzu suna samun cunkoson motoci. Kasuwar kuma na bukatar wurin tara shara. Kana suna neman a ingatawa kasuwar tsaro.

Ga rahoton Mahmud Kwari.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG