Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbaci Shirin Tsagaita Wuta A Aleppo Ya Tsaya-MDD


Hare-haren sama sun rugurguza birnin Aleppo dake kasar Siriya
Hare-haren sama sun rugurguza birnin Aleppo dake kasar Siriya

Rashin tabbaci daga bangarorin dake fada da junansu a birnin Aleppoi ya tilasatawa Majalisar Dinkin Duniya dakatar da kwashe marasa lafiya da aka shirya yi a yau Juma’a daga gabashin birnin.

Mai Magana da yawun ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, Jens Laerke yace “ Abin takaici baza a iya kwashe marasa lafiya da wadanda suka ji rauni a safiyar yau kamar yadda aka shirya ba, a saboda har yanzu ba’a samar da yanayin da ake bukata na yin hakan ba."

Laerke bai bayyana bangarorin da suka kasa cika alkawuran tsagaita wuta don ayyukan jinkai kamar yadda Rasha ta bayarda umurni kwana guda kafin nan ba. To sai dai kawai yace Majalisar Dinkin Duniya da al'ummar Aleppo suna cikin wani mawuyacin hali mai tsanani.

A jiya Alhamis ne Rasha taba da umarnin kara tsawon wa'adin aiki da shirin tsagaita wuta na jinkai a Aleppo da awa 24.

Shirin tsagaita wutar farko inda Syria da Rasha suka daka tar da hare hare ta sararin samaniya a ranar Talata a Aleppo, an shirya karewarshi ne jiya Alhamis da karfge 7 na maraice agogon kasar kafin a kara tsawon wa'adinsa.

XS
SM
MD
LG