Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bala'in Nukiliya Na Kara Yin Tsanani A Kasar Japan


Ana auna mutanen da aka kwashe daga kusa da masana'antar nukiliya ta Fukushima domin a ga ko alamar tururi mai guba a jikinsu, talata 15 Maris 2011.
Ana auna mutanen da aka kwashe daga kusa da masana'antar nukiliya ta Fukushima domin a ga ko alamar tururi mai guba a jikinsu, talata 15 Maris 2011.

An janye ma'aikatan dake kokarin hana injin nukiliya narkewa baki daya, bayan da tururi mai guba ya bazu da yawan gaske a masana'antar Fukushima wadda ta lalace a sanadin girgizar kasa da kuma Tsunami.

Jami’an gwamnatin kasar Japan sun ce an dakatar da kokarin da ake yi na hana wani injin sarrafa nukiliya narkewa baki daya, a bayanda yawan tururi mai guba dake yoyo a masana’antar ya kai mizanin da zai iya hallaka ma’aikatan dake wurin.

Babban kakakin gwamnati, Yukio Edano, ya fadawa ‘yan jarida cewa yawan tururi mai guba dake yoyo a masana’antar nukiliya ta Fukushima da ta lalace, ya cira sama sosai da misalin hantsin yau laraba agogon kasar. Yace an kwashe sauran ma’aikatan dake wannan masana’anta zuwa wani wurin da babu hatsari, a saboda irin mummunar illar dake tattare da karuwar tururin mai guba.

Edano, yace yawan tururin mai guba ya ragu kadan, kuma jami’ai su na auna shi a kai a kai domin gano lokacin da ma’aikata zasu iya komawa cikin masana’antar ba tare da fuskantar hatsari ba.

A yau laraba da sanyin safiya, an ga wani abu mai kama da farin hayaki yana fitowa ta bututun daya daga cikin injunan nukiliya na wannan masana’anta, wadda ta samu nakkasa a sanadin girgizar kasa da munanan igiyoyin ruwan teku da suka biyo baya. Edano yace jami’ai su na bin diddigin musabbabin wannan hayaki, amma yace a bisa dukkan alamu hayakin ya samu asali ne daga tururin dake fitowa daga wani kundun injin nukiliya da ya fashe a daya daga cikin injunan dake wannan masana’anta.

Gwamnatin Japan tana kokarin kaucewa abkuwar mummunan bala’in nukiliya a wannan masana’anta da ta gurgunce. An kwashe dubban mutane daga wuri mai fadin kilomita 20 a kewayen wannan masana’anta. Haka kuma, hukumomi su na aikewa da likitoci da kayayyakin bukatun gaggawa ga dubban mutanen da ke zaune ba su da abinci ko ruwa ko matsuguni a bayan girgizar kasa mai karfi da munanan igiyoyin ruwan teku da suka wanke garuruwa da kauyuka.

A jiya talata, gidan telebijin na NHK na Japan ya ambaci jami’an gwamnati su na fadin cewa an tabbatar da mutuwar mutane dubu 3, amma kuma akwai wasu mutanen su fiye da dubu 10 wadanda suka bace, ana kuma fargabar cewa sun mutu ne.

XS
SM
MD
LG