Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Hallaka Mutane a Mogadishun Kasar Somalia


የአል-ሸባብ ታጣቂ
የአል-ሸባብ ታጣቂ

‘Yan sanda a Mogadishu babban birnin kasar Somalia sun ce wani bam da ya tarwatse a wata mota ya kashe mutane da dama a wani babban titi mai yawan zirga-zirgar jama’a.

Sannan bayan tashin bam din kuma sai aka bi da harbin kan mai uwa da wabi da bindiga, mafi yawanci wadanda ake kyautata zaton sun jikkata fararen hula ne.

Kamfanin dillancin labaran Reaters sun rawaito cewa, wani bangare na wasu rukunin kasuwar da ke kusa da wajen ya tarwatse.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai shugabanin gwamnatin tarayya dana yankuna suka idar da zaman tattaunawar kwanaki uku na yadda za a tsara zabe ingantacce a shekarar 2016 mai zuwa.

Shugabannin dai sun kuduri aniyar rushe gwamantin kasar, amma ba su haramtawa shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmud da membobin majalisar kasa guda 275 tsayawa takarar shugabanci ba.

XS
SM
MD
LG