Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi Yau Lahadi A Wata Majami'ar Katolika A Jos


'Yan sandan hukumar SSS mai tsaron cikin gidan Najeriya
'Yan sandan hukumar SSS mai tsaron cikin gidan Najeriya

Hukumomi sun ce mutane akalla 6 sun mutu, yayin da aka fara kai hare-haren ramuwar gayya a garin Mai Adiko dake kusa da nan

Wani da ake kyautata zaton dan harin bam na kunar bakin wake ne ya kai farmaki kan wata majami’ar Katolika dake Jos a Najeriya ya kashe mutane akalla 3.

Wannan lamarin ya faru ne yau lahadi a kofar majami’ar St. Finbar dake garin na Jos inda aka saba ganin tashin hankali a tsakanin Kirista da Musulmi.

Ma'aikatan gaggawa suka ce wata motar da aka cika da bam ta tarwatse a lokacin da ta doshi wannan majami'a dake unguwar Rayfield a bayan garin Jos.

Wakiliyar Muryar Amurka a Jos, ta ce matasa a fusace sun toshe hanya su na kona tayu, kuma akwai rahotannin cewa an kai hare-haren ramuwar gayya a kan wasu da ake zaton Musulmi ne.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da mutane biyun da ake kyautata zaton maharan ne, da kuma wasu mutane biyu a kan babura da aka kai musu farmakin daukar fansa.

Ma’aikatan jinya sun garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti, yayin da masu bincike suka rufe wurin.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan farmakin, amma kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin wasu hare-hare irin wannan a can baya, ciki har da harin ranar 26 ga watan fabrairu da ya kashe mutane akalla 6 a majami’ar COCIN ta Jos.

XS
SM
MD
LG