Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamanga Tukur Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Taron PDP


Sakataren Majalisar amintattun jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin, yace taron nasu bai ma tattauna batun saukar Bamanga Tukur, shugaban jam'iyyar mai fuskantar suka ba.

Sakataren Majalisar Amintattun jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya, sanata Walid Jibrin, yace taron majalisar kolin jam'iyyar da aka gudanar jiya alhamis a Abuja, bai ma tabo batun shugaban jam'iyyar Bamanga Tukur ba, kamar yadda aka yi ta rade-radin cewa za a tilasta masa sauka.

Sakataren yace abu guda da suka tattauna kawai, shine batun jami'an jam'iyyar wadanda hukumar zabe ta Najeriya ta ayyana cewa ba a zabe su bisa ka'ida ba, kuma Bamanga Tukur ba ya cikin wadannan mutanen.

Ya kalubalanci masu cewa a cire Bamanga Tukur, yana mai fadin cewa ai idan akwai masu neman ya sauka, sai su zo gaban taro irin wannan su fadi haka. Yace babu wata hujja da wasu mutanen dabam zasu matsa musu lamba a kan su kori shugabansu.

Haka kuma yayi watsi da ikirarin cewa akwai wasu gwamnonin jam'iyyar PDP wadanda suka lashi takobin sai sun ga bayan shi Bamanga Tukur, inda yace wani ya fito yace yana son Bamanga ya sauka wani abu ne dabam, bin ka'ida kuma dabam ne. Yace majalisarsu ta bi ka'ida kan wannan batun.

Ga bayanin Sanata Walid Jibrin a tattaunawarsu da Nasiru Adamu el-Hikaya.

Sanata Walid Jibrin, Sakataren Majalisar Amintattun Jam'iyyar PDP Kan Taronsu A Abuja - 2:31
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG