Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ce An Manta Da Mu Ba – Turai ‘Yar’adua


Turai Yar'Adua, wife of late President Umaru Yar'Adua, stands with Patience Jonathan as her husband's body is loaded into a plane to be transported for burial in Katsina.
Turai Yar'Adua, wife of late President Umaru Yar'Adua, stands with Patience Jonathan as her husband's body is loaded into a plane to be transported for burial in Katsina.

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya Hajiya Turai ‘Yar’adua, ta musanta rahotanni da ke nuna cewa ta ce an manta da su bayan mutuwar mai gidanta.

A wata hira da ta yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Turai ta ce ita ba ta san inda labarin ya samo asali ba.

Wasu kafofin yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa iyalan tsohon shugaban kasar suna korafin cewa an manta da su, amma Turai ta ce labarin ba shi da tushe ballantana makama.

“Wallahi ba ni na yi ba, ni ban taba hira da kowa ba, kuma ban yi magana da kowa ba.” Inji Turai.

Turai ta kara da cewa, babban abu garesu shi ne duk inda ta ratsa sai mutane sun yi ta ma mai gidanta addu’a, saboda haka ba su da ra’ayin cewa an manta da su.

“Ka wuce a yi ma mutum addu’a a ce Allah ya ji kan Mutawalle shine babban abu, mu bamu da wani korafi Alhamdulillahi, mun gode wa Allah.” Turai ta ce.

saurari cikakkiyar hirar Hajiya Turai 'Yar'adua da Aliyu Mustapha na Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG