Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Dake Gaban Hukumomi da Shuwagabanin Al’uma


Wasu mutane kennan da tashe-tashen hankula ya raba da gidajensu.
Wasu mutane kennan da tashe-tashen hankula ya raba da gidajensu.

Yayin da dakarun Sojojin Najeriya, ke cigaba da kwato garuruwan dake hannun mayakan Boko Haram, a arewacin jihar Adamawa, wani batu dake gaban hukumomi da shuwagabanin al’uma, shine na maida jama’a suwa gidajensu.

Abunda tuni har wasu ‘yan siyasa, suka fara taimakawa Barrister Sunday Joshua, wani dan asalin yankin Mubi, kuma dan jam’iyyar PDM, ya bayyana dalilansu na maida jama’a, gidajensu.

Barrister Sunday, yace “ yadda nake maka magana mahaifi nama na rasa shi a sanadiyar wannan aika-aika na Boko Haram, mu iya sanin mu babu Gwamnati anan mudai kawai Allah ne madafarmu, Gwamna muna dashi kuma daga Madagali, yake bai je wuraramu ba baiyiwa kowa jajeba.”

Gwamnan jihar Adamawa Mr. Bala James Ngillari, ta bakin kakakinsa Mr. Pinas Elesha, yace” Akwai kwamiti dake kula da batun agaji wanda za’a taimakamasu da komai sakataren Gwamnatin jihar ke jagorantar kwamitin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:02 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG