Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bisa Ga Alamu Rikicin APC A Jihar Adamawa Yana Habaka


APC logo
APC logo

Taron jam'iyyar APC da aka yi a fadar gwamnan Adamawa ya jawo cecekuce

Taron jam'iyyar APC da aka yi a fadar gwamnatin jihar Adamawa ya haddasa wasu jigajigan jam'iyyar a jihar.

Janaral Buba Marwa tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar kujerar gwamnan Adamawa a zaben da ya wuce da Marcus Gundiri sun kauracewa taron. In ji ta bakin Janaral Marwa ya ce abun da gwamnan jihar Murtala Nyako ya yi shi da mukarrabansa tamkar sun shigo gidansu ne su kwace masu abinci. Ya ce wadanda suke ba gwamnan shawara basa bashi shawarar kwarai. Ya ce babu wani da zai shigo jam'iyyar ya mayarda ita tashi shi kadai.

To sai dai gwamna Nyako ya ce su ba baki ba ne a jam'iyyar APC domin duk wasu jam'iyyu babu su. Kowa ya zo ne a taru a gina sabuwar jam'iyyar APC. Don haka ba daidai ba ne a ce su baki ne.

Shi ko tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ACN Nuhu Ribadu wanda ya halicci taron ya ce PDP ce take haddasa rikici domin ta wargaza APC. Ya ce ba zasu samu abun da suke nema ba. Ya ce babu baraka a jam'iyyar. Ya ce idan gida ya girma to dole ne a samu dan tashin hankali. Ya ce idan an zauna za'a daidaita.

Amma tuni wasu kungiyoyi irin su "Neighbor to Neighbor" da suka yi ruwa suka yi tsaki suka tallatar da PDP har aka zabi shugaba Jonathan suka canza sheka zuwa APC. Shugaban kungiyar Aljhaji Ahmed Lawal ya ce sun bar PDP domin rashin adalci da jam'iyyar ta shuka da yiwa mutane wulakanci. Ya ce jama'a ke cin zabe. Duk mutanen kirki masu adalci da bakin fada a ji sun bar PDP sun koma APC.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz
XS
SM
MD
LG