Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bolivia ta Amince da Halalcin Kasar Falasdinu


Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

Gwamnatin kasar Bolivia ta fito fili a hukumance ta bayyana goyon bayan ta ga kasar Falasdinu mai zaman kan ta

Gwamnatin kasar Bolivia ta fito fili a hukumance ta bayyana goyon bayan ta ga kasar Falasdinu mai zaman kan ta, a wani matakin bin sahun makwaftan ta, Brazil da Argentina, wadanda su ka bayyana na su goyon bayan a farkon wannan wata.

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales ya fada a jiya laraba cewa kasar shi ba za ta iya ci gaba da dane hannu ta yi zaman jira ba, ganin irin matsalolin da Falasdinu ke fuskanta na keta haddin bil Adama da na yankin da kuma na ‘yancin kai. Wani jami’in ma’aikatar harakokin wajen kasar ya tabbatar da cewa a jiya laraba gwamnatin kasar Bolivia ta aika da wasika zuwa ga shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, wadda a cikin ta, gwamnatin ta kasar Bolivia ta bayyana ma ta goyon bayan ta.

Ita ma Venezuela ta amince da kasar Falasdinu mai zaman kan ta, a yayin da Uruguay ta bada sanarwar cewa ta na shirin bayyana ta, ta amincewa a shekara mai zuwa.

Lokacin da Brazil da Argentina su ka amince da kasar Falasdinu mai zaman kan ta, kuma mai cikakkun kan iyakokin ta kamar yadda su ke kafin shekarar 1967, Amurka da Israila sun yi ahir da shawarar, wadda suka bayyana a matsayin mai maida hannun agogon baya kuma mai cike da lahani.

A makon jiya majalisar wakilan Amurka ta amince bai daya da wani kudirin da ya ki goyon bayan yin gaban kai a ayyana kasar Falasdinu mai zaman kan ta. Tarayyar Turai ta yanke shawarar cewa za ta tsaya har lokacin da ya dace ta goyi bayan aiyanawar yin gaban kan.

Hukumar mulkin kan Falasdinawa ta fara tuntubar daidaikun kasashe domin ta samu goyon bayan su a kan wannan batu.

XS
SM
MD
LG