Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Fashe A Kofar Sakatariyar Garin Maiduguri


Ma'aikatan Agaji
Ma'aikatan Agaji

Yau ranar Alhamis da missalin karfe 12:40 ne aka sami tashin wani bom a bakin sakatariyar garin Maiduguri, wanda ya hallaka mutane 3 da raunata wasu 6.

Wannan tashin bom din ya farune a dai dai lokacin da ake tantance ma’aikata a sakatariyar, wanda kuma ya kasance karo na farko da aka sami irin wannan tashin bon a wannan ma’aikata. Tuni dai gwamnan jihar Borno da sauran jami’an tsaro suka ziyarci wannan wuri, haka kuma sun ziyarci asibitin da aka kwantar da mutanen da suka sami raunuka.

Rahotanni dai na cewa bom din ya tashi a dai dai inda jami’an yan Sanda ke bincikar ababawan hawa dab da shiga sakatariya. Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya tuntubi kwamishinan yan sandan jihar don neman karin bayani, sai dai kwamishinan bashi da hurumin yin magana domin yana cikin wani taro.

A jiya ne rundunar sojan Najeriya, ta fitar da wata sanarwa dake cewa ta kawar da yiwuwar kunar bakin wake a unguwar Silimanti da wani yayi kokarin shigowa da shi.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG