Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashi a Jihar Bauchi


Bom ya fashe a Bauchi. (File Photo)
Bom ya fashe a Bauchi. (File Photo)

Da dumi duminta, wani bom ya tashi a wata kasuwa a jihar Bauchi amma ba a san adadin wadanda suka mutu ko jikkata ba.

Kasa da sa’o’I goma sha biyu bayan tashin bom din da ya faru a tashar motar jihar Gombe, an kara samun fashewar wani bom din a makwabciyar jihar ta Gombe, a tsakiyar kasuwar garin Bauchi yayinda ake ta shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti.

A halin da ake ciki dai babu wani bayani akan mutuwa ko rauni, amma wakilin muryar Abdulwahab Mohammed ya shaida ma muryar Amurka cewa kakakin hukumar ‘yan sanda Haruna Mohammed, ya ce sun tura jami’an tsaro da ‘yan kwana-kwana wurin.

Babu dai cikakken bayani akan ko wani ya dauki alhakin harin ko kuma an kama wani, ana nan dai ana bincike akan lamarin. Amma ana kyautata zaton cewa ‘yan kungiyar boko haram ne suka kai harin.

Bom ya Tashi a Jiahar Bauchi - 3'06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

XS
SM
MD
LG