Accessibility links

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wani mummunan hari a jihar.

Harin an kai shi ne da maraicin jiya Asabar inda aka kashe mutane da dama a garin Dalori da ke karamar hukumar Kwanduga.

Jihar Borno wacce daga nan ne matsalar Boko Haram ta samo asali ta fi kowace jiha fama da matsalar tsaro.

Babu takaiman adadin mutanen da suka mutu ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, amma wasu majiyoyi na cewa mutane sama da 50 sun halaka yayin da aka kona gidaje da dukiyoyi da dama.

Dubban mutane hare-haren kungiyar ya halaka yayin da fiye da mutane miliyan daya suka fice daga gidajensu domin kaucewa rikicin.

Sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sha alwashin shawo kan matsalar tsaron tun da ta karbi ragamar mulkin kasar a watan Mayun bara.

Domin jin karin bayani dangane da wannan hari da aka kai a garin na Dalori, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:

XS
SM
MD
LG