Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Britaniya Zata Ninka Gudumawarta Ga Yaki Da Cutar Polio


Wata jami'a ta Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya tana diga ma wani jariri maganin rigakafin cutar Polio a Mogadishu, Somaliya.
Wata jami'a ta Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya tana diga ma wani jariri maganin rigakafin cutar Polio a Mogadishu, Somaliya.

Firayim Minista Cameron ya bi sahun Bil da Melinda Gates wajen kiran da a kammala yakin da aka faro da cutar shan inna ta Polio

A yayin da yake yin misali da irin gagarumar nasarar da aka samu ta allurar rigakafin cutar shan Inna ko Polio, firayim minista David Cameron na Britaniya ya bi sahun Bill da Melinda Gates wajen kira ga shugabannin duniya da su dage a kammala wannan yakin da aka faro.

A karshen watan da ya shige ne dai firayim ministan na Britaniya yace Britaniya zata ninka yawan gudumawar da ta ke bayarwa a yanzu ga yaki da cutar ta Polio.

Mr. Cameron ya bayyana kudurin Britaniya na ganin an yi allurar rigakafin cutar ta Polio ga karin yara su miliyan 45. Har ila yau yayi kira ga sauran masu bayar da agaji da su tallafawa Shirin Yaki da Cutar Polio ta Duniya. Yace matsalar kudin da ake fuskanta a yanzu, ba zai hana a yi abinda ya dace ba.

A cikin shekaru 20 da suka shige, an rage yawan masu kamuwa da cutar Polio da kashi 99 cikin 100 a fadin duniya. Kasashe biyun da suka fi fama da wannan matsala, Najeriya da Indiya, su ma a shekarar 2010 sun samu nasarar rage yawan masu kamuwa da wannan cuta da kashi 95 cikin 100. Amma idan har ba a kawar da ita gaba daya ba, cutar ta Polio zata ci gaba da zama barazana ga yara a ko ina a duniya.

Sabuwar gudumawar da za a bayar zata yi kokarin kawar da wannan cuta baki dayanta. Kungiyar Rotary International ta taka muhimmiyar rawa a wannan gwagwarmayar. Mr. Cameron da Mr. Gates duk sun jinjinawa 'ya'yan kungiyar ta Ritary wadanda suka fito da gudumawar dala miliyan dubu daya da dari daya daga aljihunsu domin yakar cutar Polio.

XS
SM
MD
LG