Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Ce a Binciko Masu Karkata Akalar Abincin ‘Yan gudun Hijra


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ba da umurnin gudanar da bincike, domin gano wadanda ke karkata akalar kayan abincin da ake aikawa masu gudun hijra a jihar Borno.

Dubun dubatar mutane ne ke jibge a sansanoni daban daban a duk fadin jihar ta Borno, wadanda suka tsere daga gidajensu domin gujewa rikicin Boko Haram.

Kungiyar ta Boko Haram ta kwashe kusan shekaru da dama ta na kai hare-hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya da ma kasashe ketare.

A ‘yan makwannin an samu korafe-korafen cewa wasu daga cikin wadanda ake dorawa alhakin raba kayan abinci da gwamnati da kungiyoyi ke aikawa ‘yan gudun hijrar suna sace kayan abincin.

Wannan lamari kuma ya sa a makon da ya gabata ‘yan gudun hijrar da dama suka yi zanga zanga.

Matsalar karancin abinci musamman mai gina jiki, ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a sansanonin ‘yan gudun hijrar, musamman ma kananan yara.

Domin jin fashin baki kan wannan batu, saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Umar Faruk Musa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

XS
SM
MD
LG