Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Charles Taylor da Lauyansa Sun Fice Daga Kotu A Fusace


رنگا رنگ ملبوسات کے ساتھ چہروں پر مزاحیہ نقش و نگار بنا کر یہ لوگ گودالوپ دیوی کو خراج عقیدت پیش کرنے جا رہے ہیں۔
رنگا رنگ ملبوسات کے ساتھ چہروں پر مزاحیہ نقش و نگار بنا کر یہ لوگ گودالوپ دیوی کو خراج عقیدت پیش کرنے جا رہے ہیں۔

Wannan lamari ya faru a bayanda alkalan kotun suka ki yarda su karbi takardar kariyar da lauyan tsohon shugaban na Liberiya ya gabatar

Tsohon shugaba Charles Taylor na kasar Liberiya, da lauyansa sun shura takalma suka fice daga shari’ar aikata laifuffukan yakin da ake yi ma tsohon shugaban, a bayan da alkalan kotu suka ki yarda su karbi takardar cikakken bayanin kariyar da lauyan ya gabatar.

A yau talata alkalan kotun ta musamman mai bin kadin laifuffukan yaki a kasar Saliyo suka ki yarda da wannan rubutacciyar takardar kariya a saboda wa’adin gabatar da ita ya shige. Daga nan sai lauya Courtenay Griffiths ya ki bin umurnin da alkalai suka ba shi na ya ci gaba da zama a cikin kotun. Daga bisani kuma ya bayyana wannan shari’a baki dayanta a zaman ta bagu kawai. A can baya, Griffiths ya kalubalanci ‘yancin da kotun ke da shi na yin shari’a tsakani da Allah, yana mai kafa hujja da wasu bayanan da aka samu cikin wasu takardun diflomasiyya na sirri na Amurka wadanda kungiyar Wikileaks ta fallasa.

Mr. Taylor ya ci gaba da zama na wani dan lokaci a cikin kotun yau talata a yayin da masu gabatar da kararraki suka kammala bayanan hujjojin da suka gabatar kansa. Daga bisani da aka tafi hutun cin abinci da mike kafa, sai tsohon shugaban ya ki komowa cikin kotun.

Masu gabatar da kararrakin sun ce Mr. Taylor ya samar da makamai ga ‘yan tawaye a lokacin yakin basasar Saliyo, ya kuma umurce su da su ci zarafin jama’a a kokarinsa na wawushe duwatsun Daiman na kasar. Tsohon shugaban na Liberiya yana fuskantar tuhume-tuhume 11 ciki har da kisan kai da gana azaba tare da yin amfani da yara a zaman sojoji. Charles Taylor dai ya musanta aikata wadannan laifuffukan.

XS
SM
MD
LG