Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Boko Haram Sun Tsananta


Yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Niger da Chadi domin tattaunawa da shugabannin kasashen biyu, kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a Najeriyar.

Hare-haren sun fi shafar jahohin Borno ne da Adamawa inda rayukan mutane da dama suka salwanta.

Ko jiya sai da aka samu wani tashin bam a wajen binciken ababen hawa daf da kofar shiga barikin Maimalari wanda aka ce ya jikkata mutane da dama.

Sai dai an samu rahotanni masu karo da juna yayin da ake cewa wannan bam ya tashi ne a cikin wata mota kirar Sharon wasu kuma na cewa ya tashi ne cikin motar itace.

Sai dai batun da ya tabbata shine an samu tashin bam din kuma ya hallaka mutane da dama, harin da wasu ke cewa.

Koma menene dai wannan lamari akwai abin dubawa ganin yadda hukumomin tsaron ke bugun kirjin cewa suna samun nasara akan wadannan mahara.

Ga karin bayani a wannan rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG