Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Shida - Yadda Ake Ganowa Da Jinyar Maleriya


Kwararren likita yana bincike kan kwayar cutar Malaeriya a wani asibitin kasar Kenya a watan Nuwambar 2010.
Kwararren likita yana bincike kan kwayar cutar Malaeriya a wani asibitin kasar Kenya a watan Nuwambar 2010.

Ganowa tare da yin jinyar cutar maleriya da wuri su na rage tsananin cutar da kuma mace-macen da ta ke haddasawa.

Ganowa tare da yin jinyar cutar maleriya da wuri su na rage tsananin cutar da kuma mace-macen da ta ke haddasawa. Haka kuma, su na rage yaduwar wannan cuta.

Jinyar cutar maleriya mafi nagarta a yanzu, musamman wadda kwayar halittar cutar maleriya ta P. Falciparum ta janyo, ita ce ta yin amfani da gaurayen magungunan da aka hada da sinadarin Artemisinin (ACT a takaice).

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta bayar da shawarar cewa a tabbatar da cewa kwayar cutar maleriya ce a jikin mutum kafin a fara yi masa jinyar cutar. Ana iya gudanar da bincike a tabbatar da kasancewar kwayar cutar maleriya a jikin mutum cikin ‘yan mintoci kadan. Bai kamata a fara ba da mutum maganin cutar maleriya domin ya nuna alamun cutar kawai ba, har sai an gwada an ga cewa lallai cutar ce domin akwai wasu cututtukan masu alamu kamar ita Maleriya. Za a iya fara bayar da maganin maleriya ne kawai idan har babu hanyar da za a iya yin gwaji a tabbatar da ko akwai kwayar cutar a jikin mutum.

DAKUSHEWAR KAIFIN MAGUNGUNAN MALERIYA

Dakushewar kaifin magungunan yaki da cutar maleriya ta yadu sosai kuma da sauri, abinda ya gurgunta kokarin yaki da wannan cuta.

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Shida - Yadda Ake Ganowa Da Jinyar Maleriya
Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Shida - Yadda Ake Ganowa Da Jinyar Maleriya

Idan an sha magani kwaya daya tak na sinadarin Artemisinin, akasari marasa lafiya su kan dakatar da shan maganin kafin wa’adi a saboda bacewar alamun cutar maleriya daga jikinsu. Wannan yana nufin sun yi jinyar cutar rabi da rabi ne a saboda akwai raguwar kwayoyin cutar ta maleriya a cikin jininsu. Idan ba bayar da wani maganin a hade da na farko kamar yadda ake yi karkashin tsarin ACT ba (watau bayar da gaurayen magunguna hade da na sinadarin Artemisinin), kwayoyin cutar maleriya da suka rage a cikin jini suka fara samun juriya zasu shiga jikin sauro idan ya ciji maras lafiyar, su yada ga wani mutum dabam. A saboda haka babban abinda ke janyo kushewar kaifin maganin yaki da cutar Maleriya na Artesiminin shi ne shan magani mai sinadari kwaya daya tak kawai a cikinsa.

Idan har dakushewar kaifin maganin cutar maleriya na Artemisinin ta yadu a yankuna masu yawa, kamar yadda ya faru ga magungunan yaki da Maleriya irinsu Chloroquine da Sulfacoxine-Pyrimethamine (SP), lafiyar jama’a a fadin duniya zata yi illa sosai a saboda a yanzu haka babu wani maganin da ake da shi na yaki da cutar maleriya a nan kusa.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya tana bayar da shawarar sanya idanu domin gano yadda kaifin magungunan yaki da cutar maleriya ke dakushewa, tana kuma tallafawa kasashen wajen karfafa kokarinsu a wannan fanni mai muhimmanci na kare lafiyar al’umma.

XS
SM
MD
LG