Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Karbar Abin Goro A Dalilin Dokar-Ta-Baci


Jama'a a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, sun ce 'yan sanda su na takura musu wajen karbar dubbai a hannunsu, amma kakakin 'yan sandan yace a'a

Jama'a na garin Yola, hedkwatar Jihar Adamawa, sun ce 'yan sanda su na fitowa tun kafin lokacin da aka sanya na hana fita su kakkafa shingaye, su na neman duk wanda suka tsare da ya ba su cin hancin abinda ya kama daga dubu uku zuwa dubu 5.

Wasu al'ummar da suka tattauna da wakilin sashen Hausa, Ibrahim Abdulaziz, sun ce lamarin yayi tsananin da har su kan bar abubuwan da suke yi kafin cikar wa'adin zama a waje, domin su garzaya gidajensu.

Amma rundunar 'yan sandan Jihar ta ce ba ta da masaniya, ta kuma roki jama'a da su kai rahoton duk wani dan sandan da ya nemi cin hanci daga wurinsu. kakakin rundunar, DSP Mohammed Ibrahim, ya roki jama'a da su daina bayarwa koda an tambaye su, har ma yace bayar da cin hancin ma laifi ne.

Su kuma sojojin da aka dora ma alhakin tabbatar da aiki da dokar ta baci, sun roki jama'a ne da su tabbatar su na bin dokokin da aka kafa musu.

Wakilin na VOA Hausa yayi tattaki zuwa jikin wani ofishin 'yan sanda na yanki a Yola, daga inda ya aiko da wannan rahoto da za a ji...

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG