Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CIKAR SARKIN MUSULMI SHEKARU 10 BISA MULKI: AN YI HAWAN DABA NA MUSAMMAN A SAKKWATO


Bukukuwa a Fadar Sarkin Musulmi.
Bukukuwa a Fadar Sarkin Musulmi.

Magabata daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarci bukin cika shekaru 10 bisa mulki da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar Na Uku ya yi, abin da aka ce ya nuna hadin kan 'yan Najeriya.

Gwamnonin jahohi sun bi sahun sarakunan gargajiya wajen shiga irinta sarauta; sannan manyan magabata ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wasu manyan ‘yan siyasa, sun hallarci hawan daban, wanda shi ne babi na karshe a bukukuwan cika shekaru 10 kan karagar mulki na Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya ce bukin, wanda ya hada magabata mabiya addinai daban-daban, wata hanya ce ta kara hada kan Najeriya. Sarkin Musulmin ya kula cewa mutane daga sassa daban-daban na kasar sun hallara. Don haka ya kalubalanci masu yinkurin raba kan Najeriya.

Sarkin Musulmin ya kuma yaba ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari saboda yaki da ta’addanci da almundahana da kuma irin nasarorin da yak e samu. Ya kuma jaddada cewa su a nasu bangaren za su cigaba da bayar da hadin kai ga Shugaban Kasa Buhari baya kuma da kokarin da za su cigaba da yi na ganin an zauna lafiya a Najeriya.

Ga wakilinmu a Sakkwato, Murtala Faruk Sanyinna, da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

XS
SM
MD
LG