Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciwon Zuciya Na Kashe Fiye da Mutane Miliyan 17 Kowace Shekara a Duniya


Samfarin zuciyar mutum.
Samfarin zuciyar mutum.

Yau Litinin ce ranar zuciya ta duniya inda kwararru suka bayyana cewa cututtuka dake da alaka da zuciya suna sanadiyar mutuwar mutane fiye da miliyan 17 a duk fadin duniya kowace shekara.

Hakan yasa majalisar dinkin duniya ta kebe ranar 29 ta kowace watan Satumba a matsayin ranar fadakar da al'umma akn hanyoyin da za'a bi a gujewa kamuwa da ciwon zuciya.

Farfasa Solomon Sule Dan Bauchi likitan cututuka da suka shafi hakarkari da zuciya a asibitin koyaswa na Jami'ar Jos yayi bayani akan yadda ake kamuwa da cutar.

Yace kamar mace dake da juna biyu idan ta samu ciwo yana iya taba yaron cikinta wanda kuma ka iya taba zuciyar yaron. Idan kuma mutum ya manyanta yana iya samun hawan jini. Akwai wasu abubuwan kuma da ka iya kawo ciwon zuciya. Giya na iya kawo ciwon zuciya. Ciwon suga shi ma yana iya kawo ciwon zuciya. Akwai alamomi da yawa. Kasala da rashin karfi na cikin alamomin. Idan mutum na tafiya ba zai tafi da nisa ba sai ya gaji da kuma nunfashi. Wani zubin kuma a cikin barci sai mutum ya ji kamar ya shake domin nunfashi baya tafiya yadda ya kamata.Kafafuwa da fuska na iya kumbura

Dangane da yadda za'a gujewa ciwon zuciya Farfasa yace idan mace nada juna biyu kuma tana zuwa gwaji to za'a gane a yi magani. Wanda ya manyanta ya dinga zuwa ana gwadashi wajen likita. Ya kuma rage cin gishiri. Ya dinga attisahi ko motsa jiki. Ya rage cin maiko. Ya gujewa shan taba. A rage kiba. A rage soye soyen abinci. A dingi cin ganye da 'ya'yan itace.

Ga karin bayani daga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG