Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Clinton da Sanders Ka Iya Cimma Daidaito Kafin Taron Kolin Jam'iyyar Democrat Watan Gobe


Hillary Clinton ta Jam'iyyar Democrat
Hillary Clinton ta Jam'iyyar Democrat

Yayinda Hillary Cliinton take ciga da murnar nasara da ta samu akan abokin hamayyarta, Bernie Sanders, 'yan takaran biyu suna kusa da cimma abun da 'yan jama'iyyar ke fatan zai zama sasantawa tsakaninsu lamarin da zai hada kawunan 'yan jam'iyyar kafin taron kolinta watan gobe.

Hillary Clinton ta ayyana kanta a matsayin wadda ta lashe zaben fidda gwani na jam'iyyarta bayan da ta lashe zabukan fidda da gwani na jihohin California, New Jersey, New Mexico da South Dakota lamarin da ya sa ta zama mace ta farko a tarihin Amurka da zata zama 'yar takarar shugaban kasa ta wata babbar jam'iyyar kasar.

Duk da nasarar da Hillary Clinton ta samu abokin hamayyarta bai nuna alamar saduda ba kuma har yanzu bai aika mata da gaisuwar taya murna ba..

A jawabin da ya yi daren Talata a Santa Monica dake jihar California, Sanders ya gayawa magoya bayansa yace ya dage sai ya hana dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump zama shugaban kasar Amurka. Wannan abun da yace shi ne kadai ya dan nuna ya amince da nasarar Hillary Clinton.

Sander ya sha alwashin cigaba da yakin neman zabe ba ji ba gani har sai ya lashe zaben fidda da gwani na karshe da za'a yi makon gobe a nan Washington D.C.

Saidai duk da ikirarin cigaba da neman shiga fadar White House, Sanders na shirin rage ma'aikatan kemfen dinsa da kusan kashi hamsin.

Sanders abokin hamayyar Hillary Clinton
Sanders abokin hamayyar Hillary Clinton

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG