Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola ta Isa Najeriya


Ma'aikatan kiwon lafiya zasu binne gawar waniw anda cutar Ebola ta kashe a Kenema, kasar Saliyo, 25 Yuni, 2014.
Ma'aikatan kiwon lafiya zasu binne gawar waniw anda cutar Ebola ta kashe a Kenema, kasar Saliyo, 25 Yuni, 2014.

Jami'an Najeriya sun ce wani mutumin da ya mutu yau jumma'a yana dauke da kwayar cutar nan ta lahira-kusa, Ebola.

Jami'an Najeriya sun ce wani mutumin da ya mutu yau jumma'a yana dauke da kwayar cutar nan ta lahira-kusa, Ebola.

Najeriya ta zamo kasa ta 4 a Afirka ta Yamma da ta tabbatar da bullar cutar Ebola, wadda ta kashe daruruwan mutane bana a kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo.

Wakilin sashen Hausa, Ladan Ibrahim Ayawa, ya ambaci jami'ai su na fadin cewa mutumin da ya mutu a sanadin cutar ta Ebola sunansa Patrick Sawyer, dan kasar Liberiya, mai shekaru 40 da haihuwa, wanda ya fara rashin lafiya lokacin da ya isa Najeriya ranar lahadi daga Monrovia.

An kai shi asibiti a Lagos, daga baya aka kebe shi wuri guda bayan da jami'an kiwon lafiya suka fara ganin alamun cutar Ebola yake fama da ita, suka kuma dauki jininsa domin yin gwaji.

A yau Jumma'a, hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce Ebola ta kashe mutane 660 a Afirka ta Yamma, wadanda suka hada da 314 a kasar Guinea, da 219 a Saliyo sai kuma 127 a kasar Liberiya.

An samu mutane kusan 1,100 wadanda suka kamu da cutar, amma wannan adadin yana iya karuwa sosai idan har wannan kwayar cuta ta fara yaduwa a Najeriya, musamman a Lagos mai mutane fiye da miliyan 17.

XS
SM
MD
LG