Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zazzabin Sauro Ya Ragu a Duniya


Sauro mai jawo zazzabi.
Sauro mai jawo zazzabi.

Yau ne ranar da hukumar lafiya ta duniya ta ware domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duk fadin duniya.

Cutar zazzabin cizon sauro dai na daya daga cikin cututtuka masu saurin hallaka jama’a a duniya. Gwamnatin tarayya a Najeriya ta bukaci a samar da gidajen sauro da maganin riga kafin zazzabin cizon sauro.

Hukumomin kiwon lafiya a jihar Neja dake arewacin Najeriya, sun ce a tsaye suke wajen yaki da yaduwar cutar zazzabin cizon sauro.

Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Neja Dr. Ibrahim Sule, yace ”akan wannan yaki na zazzabin cizon sauro munyi gwargwadon abinda gwamnatin tarayya ta bukaci ayi, wanda suka hada da samarda gidajen sauro da fadakar da jama’a akan mahimamcin tsafta, da kuma maganin riga kafi ga yara da mata masu juna biyu.”

Dangane da yaduwar zazzabin na cizon sauro a jihar ta Neja, shugaban sashen kula da yaduwa cutar malama Mary Dawaba cewa tayi ”an samu raguwar cutar da kimani kasha ashirin da biyar."

Wana rana dai da hukumar lafiya ta ware domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro nada mahimmacin gaske inji malama, Mary Dawaba.

Taken wannan rana shine na daukan mataki domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG