Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Zika Ka Iya Barkewa A Kasar Amurka


Ba abin mamaki bane idan har aka samu barkewar kwayar cutar Zika a kasar Amurka, har ta tsawon shekaru biyu musamman ma a jihohin dake gabar ruwa, a cewar wani masanin kiwon lafiya.

Dr Anthony Fauci, masanin harkokin kiwon lafiya ya shaidawa gidan talabijin na ABC ranar Asabar cewa ba zai yi mamaki ba idan aka samu bazuwar kwayar cutar a jihohin Texas, da Louisiana musamman ma da yake an samu ambaliyar ruwa a Louisiana.

Dr Fauci wanda shine shugaban cibiyar yaki da cututtukan dake yaduwa, yace yayi imanin cewa yankin dake gabar teku na iya samun bazuwar kwayar wannan cuta domin irin yanayin da Sauraye ke rayuwa a yankunan, kuma suna da tarihin mutanen da suka yi tafiye-tafiye zuwa yankin da wannan cutar take.

Yace akwai bukatar Amurka ta kwana ciki shiri koda aka samu barkewar kwayar cutar, sai kuma yace ba tabbas saboda abin da ya kira hali ko yanayin kasar ta Amurka.

Yace wata kila idan akayi sa a aka dauki matakin da za a iya dakile bazuwar ta.

Sai kuma a waje 'daya cibiyar yaki da yaduwar cututtuka ta gargadi mata da su guji zuwa bakin teku irin na Miami da Florida da yankin nan na Wynwood dake makwabtaka da Miami domin ko an samu bullar wata kwayar cutar da ake tuhuma na zika a cikin satin data gabata.

Shi dai wannan kwayar cutar wadda sauro ke haddasa ta ta bazu zuwa yankin Latin Amurka, dama wasu sassan karebiyan, sai kuma ‘yan kwanakin nan yake neman kunno kai Amurka.

Ita dai kwayar cutar ta zika bata fiye nunawa ba a jikin wanda ya kamu da ita ba, sai dai yana jefa mata masu juna biyu cikin matsanancin hali abin da har yake sawa ana haihuwar jariri da matsalar kwakwalwa.

XS
SM
MD
LG