Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alama Amurka Zata tallafawa Gwamnatin Ukraine


Nan da 'yan kwanaki Amurka zata tallafawa gwamnatin Ukraine da manyan kayan yaki

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, tace Amurka bata yanke shawara kan ko zata tallafawa Ukraine da kayan yaki ba, a fafatawar da kasar take yi da 'yan tawayenta wadanda suke samun daurin gindi daga Rasha ba. Wannan bayanin da ta yi, ya biyo bayan wani labari da wata jarida ta wallafa cewa mahukuntan kasar suna nazari kan wannan batu.

Kakakin wacce tayi magana a lokacin ganawa da manema labarai da ma'aikatar take yi ko wace rana, tace Amurka bata "bata kawar da yin amfani" da ko wane irin mataki ba, kuma har yanzu ana ci gaba da shawarwari kan mataki da kasar zata dauka.

Jaridar New York Times ranar Lahadi ta buga labarin cewa, kodashike shugaba Obama bai yanke shawara kan samarwa Ukraine muggan makaman yaki ba, gwamnatinsa tana sake "duba" batun tallafawa kasar da kayan yaki.

Jaridar ta ambaci wata majiya da bata bayyanata ba, tana cewa sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da babban hafsan hafsoshin Amurka Janar Martin Dempsey da Susan Rice, mai baiwa shugaba Obama shawarwari kan harkokin tsaro, duk basu da matsala kan batun tallafawa Ukraine da makamai.

Haka kuma jaridar ta bada labarin cewa ana shirin za'a saki wanin rahoto jiya Litinin da tsoffin manyan jami'an gwamnati suka shirya masu zaman kansu, suna kira ga Amurka ta turawa Ukraine kayan tsaro na kudi dala milyan dubu uku, wannan rahoto yana kara janyo sabbin muhawara a Washington kan batun samarwa Ukraine kayan yaki.

XS
SM
MD
LG