Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamu Akwai Baraka Tsakanin Shekau da Marwana


Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka capke
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka capke

Da Alamu Akwai Baraka Tsakanin Shekau da Marwana. Shekau ya musanta yarjejeniyar da Marwana ya bayyana sun cimma da gwamnatin Najeriya. Amma Marwana ya yi watsi da furucin Shekau.

Sau da yawa Marwana wanda ya ce yana magana da yawun kungiyar Boko Haram ya sha fitowa ya yi magana da yawun kungiyar amma sai Shekau wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar ya fito ya karyata Marwana. Makon da ya wuce Marwana ya bayyanawa duniya cewa kungiyar ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Najeriya lamarin da shugaban kwamitin neman sulhu da kungiyar na gwamnatin Najeriya ya tabbatar.

Tun ba'a yi nisa ba sai ga shi Shekau ya sake fitowa da sako inda ya musanta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnati. Maimakon hakan ya amince da kashe yaran makaranta da aka yi a Mamudo jihar Yobe ya kuma kara da barazanar dada kai hare-hare. To sai dai a wannan lokacin akwai ban-banci domin Marwana bai yi shiru kamar da can. Shi ma ya mayarda martani. Ya yi watsi da furucin Shekau ya kalubale shi ya fito ya yi hare-haren. Ya sake jaddada abubuwan da ya fada makon jiya cewa suna neman zaman lafiya. Sun yafe duk abun da aka yi masu. Su ma suna neman gafara daga al'umma duka. Ya ce a wannan watan azumi mai alfarma suna fatan kowa ya zauna lafiya a cigaba da addu'a.Ya ce yana tabbatarwa kwamitin da gwamnati ta kafa da gwamnati kanta da Musulman Najeriya su ji abun da shi Marwana ya fada su yi watsi da furucin Shekau. Ya ce a wannan karon kowanene ya ja baya zasu barshi a baya, wato kamar yana yiwa Shekau hannunka mai sanda ne.Ya ce idan gwagwarmaya Shekau zai yi shi kadai zai yi. Marwana ya ce shi ya cewa mujahidansu su bari kuma ba za'a yi ba. Ya ce shi Shekau ya fito ya ce a yi din mutane su gani. Ya kira mutane su daina saurarensa ko jin tsoron furucinsa.

Daga karshe ya tabbatar cewa nan ba dadewa ba za'a tara mujahidan bisa ga shirin zaman lafiya. Ya tabbatarwa kwamitin neman sulhu ba za'a ji kunya ba sai shi Shekau mai neman tada hankali.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG