Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Nijar Sun Yi Arangama Da ‘Yan Boko Haram a Boso


Sojoji daga Nijar da Chadi da suka kwato garin Damasak dake Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram sun gano gawarwakin mutane akalla Saba’in. Yawancinsu an yi masu yankan rago kana aka jefar dasu karkashin wata gada kamar yadda wani ganao ya shaida.
Sojoji daga Nijar da Chadi da suka kwato garin Damasak dake Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram sun gano gawarwakin mutane akalla Saba’in. Yawancinsu an yi masu yankan rago kana aka jefar dasu karkashin wata gada kamar yadda wani ganao ya shaida.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa sojojin kasar sun yi wata arangama da wasu mayakan Boko Haram da suka fada cikin barikin sojin Boso.

Ma’aikatar tsaron kasar ce ta bayyana arangamar a wata sanarwa da ta fitar, wacce ta bayyana cewa an kashe ‘yan kungiyar ta Boko Haram su goma, kana an kwace makamai da dama.

Sai dai sanarwar ta ce mayakan sun jiwa wasu sojojin kasar rauni kana an lalata wata motarsu yayin arangamar.

Mayakan sun kai harin ne da misalin karfe shida na yammacin juma'a ne aka kai harin.

Jamhuriyar Nijar ma tana fama da matsalar Boko Haram, musamman tsakanin shekara daya da rabi da ta gabata, inda sukan shiga ta yankin Diffa domin kai hare-hare.

Kasar ta Nijar na daya daga cikin kasashe da ke yankin tafkin Chadi da su ke da dakarun hadin gwiwa a rundunar tsaro da kasashen yankin suka kafa.

Domin jin cikakken bayani saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG