Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Ouattara Suna Farautar Mayakan Gbagbo A Abidjan

Tsohon shugaban kasar Ivory Coast laurent Gbagbo.
Tsohon shugaban kasar Ivory Coast laurent Gbagbo.

Mayaka masu goyon bayan shugaba Alassane Ouattara na kasar Ivory Coast ko Cote D’voire, su na farautar mayakan da suka goyi bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo a Abidjan, birni mafi girma da tasiri a kasar.

Wadanda aka kama bisa zaton cewa mayakan Gbagbo ne, ana kai su hotel mai suna Golf na Abidjan, inda nan ne hedkwatar Mr. Ouattara a tsawon watanni 4 da yayi yana gwagwarmayar mulki da Mr. Gbagbo.

A wasu sassan na birnin Abidjan, jiya talata an fuskanci kwasar ganima da harbe-harben manyan bindigogi jefi-jefi. Mayaka masu goyon bayan Ouattara su na kokarin kamo ‘ya’yan wata kungiyar matasa ‘yan tsagera masu goyon bayan Gbagbo, musamman ma shugaban kungiyar, Charles Ble Goude, wanda ya zama ministan matasa a gwamnatin Mr. Gbagbo.

Mr. Ouattara yayi kira ga dukkan mayaka da su ajiye makamansu a bayan da aka kama Mr. Gbagbo a ranar litinin. Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana rike da Mr. Gbagbo da matarsa Simone a Golf Hotel na Abidjan, karkashin kariyar majalisar.

Da farko majalisar ta ce an dauke su aka fita da su daga birnin A bidjan, amma daga bisani ta ce wannan labarin ba haka yake ba. An kama Mr. Gbagbo a bayan da ya shafe watanni fiye da hudu yana musanta cewa Mr. Ouattara ya kayar da shi a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG